Monday, 15 January 2018

DABARUN RUBUTUN FILM

MENE NE LABARI
Labari shine duk abin da mutum zaiji ko ya gani ko ya karanta wanda zai burge ko bada mamaki ko haushi ko jimami da sauransu. A takaice dai duk wani al'amari da zai ja hankalin mutum ana iya kallonsa a matsayin labari. Kamar yadda muka fada a baya,  marubuci ne ke iya zakulo labari mai ma'ana da ke iya jan hankali.

HANYOYIN SAMUN LABARI
Akwai hanyoyi da dama ake iya samun labari daga gare su. Hanyoyin kuwa sun hada da:

a.  Gani da ido
b.  Faruwar wani abu akan mutum
c.  Jin labari a kafafen watsa labarai ko daga bakunan mutane.
d.  Karatu littatafai da nazari
e.  Mafarki
f.  Bincike
g.  Tunani da hasashe da sauransu

YADDA AKE TSARA LABARI
Ya zama wajibi ga mai rubutun film ya tsara labarinsa daki-daki tare da jera abubuwan da zasu faru tun daga farko har karshe. Abu ne mai kyau marubuci ya san farkon labarinsa,  tsakiyarsa da kuma karshensa yadda zai bada maana kuma ya yi armashi.

YADDA AKE AUNA LABARIN FIM
Kowanne labarin da za a mayar da shi film sai an auna shi kan wani sikeli da masana fannin suka kira *Paradigm* wanda wajibi ne labari ya cika wadannan sikeli daidai.  Ma'aunin da ake auna labarin kuwa shi ake kira *Three Act Structure* watau shika-shikai uku na ingantaccen labarin fim.

Idan na ce ingantacce ba ina nufin labari mai nuna kyawawan dabiu ba ko sharholiya ba,  ina nufin labarin da zai dau hankali wanda mai kallo zai gaza tashi har sai ya ga karshe. Labarin da zai sa mai kallo ya kasa kauda kansa ya zama cike da dokin son ganin abin da zai auku nan gaba. Ba a so marubuci ya ba wa mai kallo damar cankar abin da zai faru nan gaba,  an fi so kodayaushe marubuci ya ba wa mai kallo ko karatu mamaki ta hanyar nuna masa wani abu da bai yi zato ba.  Wannan shi ne ingantaccen labari.

Yadda ake samar da ingantaccen labari shine matakan da ake kulla zaruruwan abubuwan da za su faru ta fuskar tambaya da amsa.  Irin wannan salo ana kiransa *What happens next* watau yin tunanin abin da zai faru daga mataki zuwa mataki. A mako mai zuwa za mu yi cikakken bayani kan wannan tsari na *three act structure*

MATAKAN RUBUTA LABARI
Rubuta ingantaccen labari yana bukatar bin wadannan matakan:

*Idea* - Watau tunani kan irin labarin da za a rubuta. Na bayyana hanyoyin da ake samun idea tun dazu.
*Pitch* - Dan takaitaccen bayani gamw da labarin. Misali, ina son bayar da labari akan malamin makaranta. Pitch dina zai zama... *Wani malamin makaranta da kudin albashi bai ishe shi ba kuma ba shi da wata sana'a ga shi matarsa ta mutu yana neman aure*

*Synopsis:* Takaitaccen bayanin labarin a dunkule inda za a fara da farkon labarin, tsakiyarsa da kuma karshensa.Yawanci baya wuce shafi daya na takardar full scalp.

*Character development:*  Samar da manyan taurari da irin dabiunsu da shekarunsu tare da duk wani bayani da zai sa a gane su cikin sauki. Za mu yi cikakken bayani akan wannan nan gaba.

*Block ko Treatment:* Wannan shi ne mataki na bi da bi na duk abin da zai faru cikin labarin daga farko har zuwa karshe. Anan ne ake fayyace *Three Act structure* wanda na ce zan yi bayaninsa mako mai zuwa Yawanci ana rubutun ne a wani kati da ake kira index card. To amma yanzu da cigaban kimiyya ya zo, ana rubutun ma a manhajojin rubutu kamar microsoft word da sauransu.

*Mu lura da kyau, wadannan matakan da na ambata a sama, ana so kowanne marubuci ya fahimcesu su kuma ya rika amfani da su yayin kowanne irin rubutun kirkira.*

RUBUTUN LABARI.
Abu na gaba shi ne rubuta labarin da aka bi matakan can da na ambata zuwa tsarin fim (Scriprwriting ko Screenwriting). Shi rubutun fim iri biyu ne; akwai wanda ake kira

 *Generic* da kuma wanda ake kira *Spec* ko *Production script*

Generic shi ne wanda marubuci ke rubutawa kai tsaye ba tare da iyakancewa ba. Kila ma marubucin ya rubuta ne a kashin kansa saboda shaawa ba tare da wani ya sa shi ba. Don haka ba a bukatar ya fayyace wasu abubuwan da babu su, misali siffanta kamannin tauraro, yanayin gida, launin mota, tsayuwar kyamera da sauransu. Sai dai idan ababen na da alaka da tasirin labarinsa.

*Spec* ko *Production* kuwa, darakta ne ke zama ya sake rubuta labarin da marubuci ya yi zuwa gwargwadon yadda yake so ya zama a aikace. Anan zai bayyana komai da komai dalla - dalla tare da bayyana irin tauraron da yake so ya zauna a labarin da kuma tsayuwar camera da awon gani da sauransu. Sai dai ya zama tilas darakta ya yi la'akari da awon labari da irin rawar da taurari suka taka. Ba abu ne mai kyau ba, marubuci ya zabi tauraro dan shekara 25, shi kuma darakta ya musanya da wani dan shekara15 ko 50. Irin wannan shi ke bata labari.

SALON RIKE MAI KALLO
Ana kiransa da *what happens next* dabara ce ake tsarawa wajen yanyanka labari yadda kafin a gama warware matsala guda an afka wata, ana warware wannan kuma sai wata mai girma ta zo. A haka har a zo karshen labarin.

Wannan salo na sa mai kallo ya bata lokacinsa  yana kallon film ba tare da ya gajiya ba. Misali, ana cikin nuna tauraron a folis  an tsare shi sai a katse a nuna wani wajen kuma can ana jiransa za a daura masa aure. Ashe wasu kuma ba sa so a daura auren da shi. Ana shawarwarin fasawa sai ga shi ya zo da waliyansa. Kun ga anan an warware matsalar folis kuma za a shiga wata. Kila ta yiwu a wajen akwai wadanda ba sa son a yi auren, kuma ya sansu. Suna ganinsa sai su firgita su shiga kame - kame. Anan mai kallo zai yi fatan ya nuna su ko ya muzanta su, to amma marubucin sai ya yi wuf ya canja akalar labarin ta wata fuska da ba a yi tsammani ba.

Idan kana son tsara labarinka daki - daki, to sai ka soma da sanin farkonsa da karshensa, daga nan sai ka shiga fadada labarinka ta hanyar *what happen s next*.

Idan mun dauki misali, labari akan fataucin miyagun kwayoyi.
 Za mu iya farawa da amsa tambayar, *me zai faru idan ana sha ko fataucin kwayoyi?*

Daga nan fa? *Me zai faru ga mahukunta wajen bincike?*

Daga nan fa? *Me zai faru idan an zo kame?*

Daga nan fa? Haka dai har ka je karshen labahrinka.

Wannan salon ma yana da amfani har ga masu rubuta novel.

Nagode

Tuesday, 19 December 2017

KANNYWOOD PARTNERS
Working as a team is very important in film industry. My partners are:

-iStudios Multimedia Ltd
-Al`umma Motion Pictures Gusau
-Prince Zango Production Nig. Ltd
-Azurfa Film Production
-Giggs International
-Digital Age Films Production
-Multipurpose Concept
-Al`rahuz Films Production
-Zamani Movies
-G25 Hausa Fulani Films
-Babaye International
-Barumi Movies
KNOW WRITER FIRST
A screenplay writer or screenwriter is a writer who practices the craft of screenwriting, writing screenplays on mass media such as films, television programs , comics or video games are based.

PROFFESSION
Screenwriting is a freelance profession. No education is required to become a professional screenwriter, just good storytelling abilities and imagination. Screenwriters are not hired employees, they are contracted freelancers. Most, if not all, screenwriters start their careers writing on speculation (spec), meaning they write without being hired or paid for it. If such a script is sold, it is called a spec script. What separates a professional screenwriter from an amateur screenwriter is that professional screenwriters are usually represented by a talent agency. Also, professional screenwriters do not often work for free; whereas amateur screenwriters will often work for free and are considered "writers in training". Spec scripts are usually penned by unknown professional screenwriters and amateur screenwriters. There are legion of would-be screenwriters who attempt to enter the film industry but it often takes years of trial-and-error, failure, and gritty persistence to achieve success. In Writing Screenplays that Sell , Michael Hague writes "Screenplays have become, for the last half of [the twentieth] century, what the Great American Novel was for the first half. Closet writers who used to dream of the glory of getting into print now dream of seeing their story on the big or small screen. Screenwriting in the film industry Every screenplay and teleplay begins with a thought or idea, and screenwriters use those ideas to write scripts, with the intention of selling them and having them produced. In some cases, the script is based on an existing property, such as a book or person's life story, which is adapted by the screenwriter. The majority of the time, a film project gets initiated by a screenwriter and because they initiated the project, the writing assignment exclusively becomes his or hers. These are referred to as "exclusive" assignments or "pitched"assignments. Screenwriters who often pitch new projects, whether original or an adaptation, often do not have to worry about competing for assignments and are often more successful. When word is put out about a project a film studio, production company , or producer wants done, these are referred to as "open" assignments. Open assignments are more competitive. In situations where screenwriters are competing for an open assignment, more established writers will usually win these assignments. A screenwriter can also be approached and personally offered a writing assignment.

Script doctoring Many screenwriters also work as full or part-time "script doctors ", attempting to better a script to suit the desires of a director or studio . For instance, studio management may have a complaint that the motivations of the characters are unclear or that the dialogue is weak. Script-doctoring can be quite lucrative, especially for the better known writers. David Mamet and John Sayles , for instance, fund the movies they direct themselves, usually from their own screenplays, by writing and doctoring scripts for others. In fact, some writers make very profitable careers out of being the ninth or tenth writer to work on a piece; in many cases, working on projects that never see exposure to an audience of any size. Many up and coming screenwriters also "ghost write" projects and allow more established screenwriters to take public credit for the project to increase the chances of it getting up.

DEVELOPMENT PROCESS OF A PROJECT
After a screenwriter finishes a project, he or she pairs with an industry-based representative, such as a producer , director, literary agent, etc.
ALLIANCE MEDIA NIGERIA
Is a media company secialized in script writting and films making, the company is headed by YUSUF MARAFA as managing director.

ESTERBLISHED
2012-Date

SERVICES
Script Writting
Producing
Directing
and some films making event

EMPLOYERS
19 Employers
ABOUT ME!

YUSUF AHMAD NAHUCHE popularly known as Marafa. I was born in 1987 at Nahuche town of Bungudu Local Government Area,  Zamfara State. My career start as an islamic student according to our culture and religios believed. I later join western education system. During this long journey of my life i have seen a challenges in this world where i meet different  peoples with different characters. Entering in to KANNYWOOD films industry open a new page of life to me, i have been there since and i steel witness the competition of life there. I thanks to Almighty ALLAH for keeping me alive, healthy and believed one.
My Projects from 2008 - Date

-Auren Zamani
-Mata Rahma                    
-Aurena Dake                  
-Matar Bahaushe
-Autar Mata
-Matar Uba
-Babbar Rana                  
-Mulkin Mallaka
-Babbar Harka
-Na Yarda Dake
-Bani Ba Aure                  
-Naira Da kwabo
-Ba Adawa                        
-Nazari
-Comandan Mata        
-Rabuwa Dake
-Dan Adam                      
-Raddi
-Dangin Juna                
-Rai Da Rabo
-Daren Wuya                  
-Ranar Aurena
-Fadi Tashi              
-Ramlat
-Farfesa                          
-Rudin Zuci
-Fatima Ko Zarah            
-Saki Kowa
-Gangar Jiki                    
-Sawun Kaddara
-Gida Daya              
-Sirrin Dake Raina
-Gidan Sarauta                
-Shine Riba
-Gidan Duniya                  
-Soyayya Da Shakuwa
-Gurguwa Mai Naira        
-So Na Jini
-Hinde                              
-Shoki
-Hanan                              
-Tsaro
-Ina Zaki Damu                
-Tsaro 2017
-Inda Ranka                      
-Ummu Sulaim
-Izaya                                
-Wani Lokaci
-Jiya Da Yau                    
-Wani Mutum
-Kana Naka                      
-Wata Mace
-Kangi                                
-Wata Sabuwa
-Kasuwar Mata                
-Mun Shaku Da Juna
-Kurciya                          
-Yancina
-Mai Kamar Zuwa        
-Yar Uwata
-Makahon So                    
-Zafin Rai
-Makauniyar Hanya      
-Zanen Dutse
-Martani                        
-Zarge
-Mata Da Miji              
-Zuciya Daya

And currently working on a series drama.

Title: Asabe

DABARUN RUBUTUN FILM

MENE NE LABARI Labari shine duk abin da mutum zaiji ko ya gani ko ya karanta wanda zai burge ko bada mamaki ko haushi ko jimami da sauransu...